Wannan Talatar Kasar Liberiya Zata Cika Shekaru 169 da Samun 'Yancin Kai"

Matar shugaban Amurka Michelle Obama da Shugabar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf

Gobe kasar Liberiya zata cika shekaru dari da sittin da tara da samun 'yancin kai daga kasar Amurka to saidai wasu na tababan ikirarin cigaba da gwamnatin kasar ke yi

A gobe Talata Liberia zata yi bikin cika shekaru 169 da samun ‘yancin kai.

Sai dai wasu ‘yan kasar na da ra’ayin cewa babu wani abun azo a gani, idan aka yi la'akari da irin matsananci hali da tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

Amma jakadan kasar a nan Amurka, Jeremia Sulunteh, ya ce, duk da cewa akwai matsaloli da ake fuskanta, kasar ta Liberia ta samu ci gaba sosai a karkashin jagorancin shugaba Ellen Johson Sirleaf.

Ya ce “a wannan shekarar, za mu yi bikin cika shekarar ne da taken “tattaro baki dayan ci gaban da muka yi, domin samar da sauyi.”.

Kuma kamar yadda kuka sani, jadawalin shekarar 2030 da aka shata, batu ne mai dogon zango da shugabar kasra ta maida hankjali akai, saboda haka, inda ga kowa ne mataki da muke dauka ya cancanci a nuna farin ciki a kai.”

Ya kuma kara da cewa, an samu ci gaba matuka ta fuskar gyara ababan more rayuwa da aka daidaita dalilin yakin basasan da kasar ta fuskanta.