Ana iya kiran wannan dalili mai lamba na 580, kada a bar yara da na’urorin zamani, don gudun irin barnar da za suyi da kan iya saka iyayen su cikin damuwa.
Domin kuwa abun da ya faru a karshen makon ga Mr. Evan Osnos, ma’aikacin tsangayar Brooking Institution a birnin New York na Amurka. Ya rubuta a shafinsa na tweeta, yana neman agaji akan wani hali da dan shi mai shekaru 3 ya sakashi.
Yaron ya dauki wayar da kokarin bude ta wanda yayi ta dannawa amma wayar na kin budewa. Bisa tsarin wayoyin kamfanin Apple a duk lokacin da kayi kokarin budewa ba dai-daiba zata baka adadin karin lokaci da zaka sake gwadawa.
Yaron yayi ta gwadawa cikin rashin sanin lambar budewa ta dai-dai, har sau bila’adadin wanda wayar bazata buduba har sai bayan mintoci 25,536,442. Kimanin shekaru 48 kenan sannan wayar zata budu a shekarar 2067.
Bayan rubutawar da yayi a shafin sa, sauran mutane sun ta bashi shawarwarin yadda zai magance wannan matsalar, da kuma kara jan hankullan mutane da su dauki matakai da suka dace, wajen hana yara amfani da na’urorin su batare da bin ka’idoji ba ko lura da abun da suke yi.