Wani Yaro Dan Kasar Guatemala Ya Mutu A Hannun Jami’an Amurka

Dan kasar Guatemala Felipe Gomez Alanzo, yaro dan shekara 8 ya mutu a safiyar ranar Kirsimeti a hannun jami'an tsaron iyakar Amurka.

Wani karamin yaro dan kasar Guatemala ya mutu a hannun jami’an tsaron Iyakar Amurka.

Felipe Gomez Alonzo, dan shekaru 8 da haihuwa ya rasu da misalin karfe 12 na safiyar ranar Kirsimeti, rana daya da aka yi jana’izar wata ‘yar shekara 7 a kauyen na a Guatemala, wacce ita ma ta rasu a inda ake tsare da bakin hauren da suka fito daga yankin tsakiyar Amurka.

Jami’an tsaron iyaka sun ce, a lokacin da suke tsare da yaron tare da mahaifinsa ne suka lura cewa yana nuna alamun rashin lafiya.

Likitoci a wani asibiti na Alamogoro da ke jihar New Mexico, sun duba Felipe, inda suka ayyana mura da zazzabi a matsayin abin da ke damunsa, hakan kuma ya sa suka ba shi magunguna.

A daren ranar Litinin Felipe ya yi ta fama da matsalar tashin zuciya, inda daga karshe ya yi ta amai.

Rahotanni sun ce daga baya an mayar da yaron asibiti, inda ya cika bayan sha-biyun dare.