Wani ya Afka Cikin Jama'a da Mota a London

‘Yan sanda a birnin London sun ce wani mutum ya afka cikin wani gungun masu tafiya da kafa da mota kafin ya banke wasu shingaye dake wajen ginin majalisar dokokin Burtaniyya yau Talata, wasu mutane sun jikkata sakamakon hakan.

Hukumomi sun ce jami’an tsaro sun kama mutumin da ya tuka motar bisa zargin aikata laifin ta’addanci. Sun kuma ce babu wani dake cikin motar kuma babu wasu makamai a cikin ta. Hukumomin sun kuma bayyana cewa shekarun mutumin na haihuwa zasu kai 20 da wani abu.

“Wannan lamarin na nuna cewa da-gangan aka aikata harin, amma dalilin sa ne bamu sani ba, “a cewar mataimakin kwamishinan birnin London Neil Basu, a lokacin da ya ke magana da manema labarai.

Mr. Basu ya kara da cewa, mutumin da ake zargi ba ya ba ‘yan sanda hadin kai a kokarin da suke yi na tantance ko shi wanene da kuma masabbabin abinda ya aikata.

Ya kuma ce bisa bayanan da masu bincike suka samu ya zuwa yanzu, mutumin bai taba yin wani abu da zai sa hukumar leken asiri ko ta yaki da ta’addanci su san da zaman shi ba.