WASHINGTON, DC —
Wata kotun soji ta samu wani sojan Issira'ila da laifin kisa, sanadiyar kashe wani ba-Falasdine nakasashshe wanda ya yi niyyar kai hari a Yamma da Kogin Jordan.
Elor Azaria dan shekaru 20 na fuskantar daurin shekaru 20 a gidan yari. Wani lokaci nan gaba za a yanke masa hukuncin.
Wannan al'amarin da ya faru a Hebron ya fito fili ne bayan da wani bidiyon da aka fitar ya nuna Azaria na harbin Abdel-Fatah al-Sharif dan shekaru 21 da haihuwa bayan da ya fadi kasa kuma ya ko ji rauni, bayan daba wuka da ya yi ma wani sojan Isira'ila.
Yayin zartas da hukuncin yau Laraba, Kanar Maya Heller ya ce, "Duk da ya ke mutumin da ya fadi kasa dan ta'adda ne, wannan ba hujja ba ce ta daukar matakin da ya wuce kima."