Fiye da masu aikata muggan laifufuka dubu biyar ne suka bayana tubarsu a kananan hukumomin ashirin da biyar dake jihar Neja, a Najeriya, kmar yadda kakakin ‘yan Sandan jihar DSP, Bala Elkana, wanda ya bayanawa jaridar Sun.
Wadanda suka bayana tubar tasu har da Yahaya Shanjijiri, mai shekaru saba’in da biyar da haihuwa wanda ya fito daga yakin Rijau, da ‘ya’yan cikinsa su goma sha hudu.
Yahaya Shanjijiri, yana daya daga cikin gawurtattun barayin jihar Neja, a lokacin da yake bayana tubarsa ga DPO, din Rijau, da sauran jami’an tsaro, yace fiye da shekaru talatin shi gawurtatcen barawo ne.
Ya kara da cewa ya daina fita sata saboda shekaru sun kama shi, amma ya kan taimakawa ‘ya’yan da horo da kuma dabaru na yadda zasu gudanar da aiyukansu na raba mutane da dukiyoyinsu.
A cewar Yahaya Shanjijiri, ya fara ‘yan dauke dauke ne tun lokacin da yake da shekaru goma, a unguwarsu daga bisani sai satar dabbobi kafin ya fara fashi.
Yahaya, yana mai cewa su kan yhi fashi sau ukku, a wata, duk fitar da su kayi nasara su kan sami Naira miliyan biyu zuwa ukku, kuma ana raba kudin gida hudu ne kasha daya na jami’an tsaro, daya na tsubbu da na ko ta kwanna saboda shara’a sa’ilin na kashi na hudu su raba a tsakaninsu.