Awowi kadan bayan tsare wani mutumi sai aka bada shi beli, akan tuhumar da akeyi mishi na cewar yaci zarafin matarshi. Duane Youd, mai shekaru 47, ya saci jirgin sama inda ya tukashi ya kuma fada cikin gidan shi da niyar kasha kansh da matar tashi.
Jim kadan bayan faduwar jirgin a karamar hukumar Payson dake jihar Utah ta Amurka, sai wuta ta kama a gidan, da misallin karfe 2:30 na dare. Mai dakin mutumin da diyanshi na cikin gidan a lokacin da hadarin ya auku.
Jami’an ‘yan sanda sun bayyanar da cewar matar mutumin da ‘ya’yan shi sun tsira, mutunmin dai ya shaidawa dan cikin shi cewar ya bar gidan ya tafi gidan mahaifiyar shi, don kada hadarin ya auka da shi.
An shaida cewar Mr. Youd, tsohon maaikacin kamfanin da ya sacema jirgin ne, kuma tsohon matukin jirgi ne. Makotan mutumin sun bayyanar cewar sunji shawagin jirgin sau biyu kamun faduwar jirgin. Mutumin dai yam utu bayan kai shi asibiti da akayi.