Wani Matashi Zai Kwashe Shekaru Ukku A Gidan Yari Dalilin Fyade

Belgium France Attacks

Babbar kotun Majistara dake garin Akure, ta yankewa wani telan matashi mai shekaru ashirin da shida da haihuwa da ya je ya samu horo a gidan yari na tsawon shekaru ukku.

Shi dai wannan matasahi an sameshi da laifin yiwa wata yarinya mai shekaru goma sha shida fyade ne.

Mai shara’a Halen Komolafe, wace ta zartar da hukuncin ta bashi zabin biyar tarar Naira dubu dari biyu, ko kuma shekaru ukku a gidan kurkuku.

Tun farko mai gabatar da kara Adebayo Ayorinde, ya fadawa kotu cewa a ranar 23, ga watan Oktoban wanna shekarar ne ya aikata laifin a lokacin da yarinyar ke tallar ayaba. Laifin ya sabawa sashe na 358 sakin layi na 37, na kundin laifuffukan jihar Ondo.