Wani Matshi Omar Mateen, Ya Hallaka Mutane 49 Da Jikkata Wasu Da Dama A Amurka

Wani matashi haihuwar Amurka mai shekaru ashirin da tara da haihuwa Omar Mateen ya hallaka mutane 49 da kuma jikkata wasu 53, da harbi da bindiga a Orlando dake jahar Florida ta kasar Amurka.

Shugaban Amurka, Barack Obama, ya bayyana harin da wannan matashi ya kai a kan wata matattarar masu auren jinsi kokuma luwadi a matsayin harin ta'addanci da nuna kin jinin wata al'umma.

Shugaba Obama ya kara da cewa wannan ya faru ne a sakamakon kasancewar kusan kowa ya mallaki bindiga a gidan sa, lamarin da yaki ci yaki cincewa a kasar.

Kamar yadda mujallar Washinton Post ta wallafa, dan takarar shugabancin Amurkar a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump ya soki Obama ne da Hillary Clinton kan cewa sun ki fitowa fili su bayyanawa mutane cewa hari ne da 'yan ta'addar musulmi suka kai.

Matashin mai shekaru 29 da haihuwa ya kai harinne da babbar bindiga da kuma karama ta hannu a lokacin da ya bude wutar. Wannan dai shi ne harin bindiga mafi muni da aka taba kai wa Amurka a tarihin kasar.