Wani Matashi Na Amfani Da Itacen Bamboo Don Samun Kudin Shiga

Ragewa, sake amfani da kuma sake sarrafawa. Wani matashi dan kasar Uganda dan kasuwa ya samar da hanyar duk wadannan abubuwa, yana gyara karafuna kekekuna da suka lalace tare da itacen gora da aka sake sarrafawa. A kokarin sa nayin haka yanzu yana samun riba da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.

A wani taron bita da yayi a babban birnin kasar Uganda Kampala, matashin dan kasuwa ya duba irin aikin da yayi da hannu. Noordin Kasoma, ya samu hanyar gyara tsofaffin karafunan kekekuna, da amfani da itacen gora, inda yake kirkirar wasu abubuwa da zai iya siyarwa domin samun kudin shiga.

Idan aka zo da batun tukin keken da aka sarrafa da itacen gora, lallai suna da sauki tukawa a gefen hanya, abu na farko shine keken da aka hada da itace gora tana da sauki sarrafawa. Saboda saukin sarrafwar da take dashi, tana rage kara idan ana tukawa musamman a gefen hanya. Duk keken da aka kirkireta da gora, tana rage kara ba kamar yadda sauran da aka kirkiresu da karfe ko dalma suke karaba.

Kasoma ya koyi yadda ake hada keken ne bayan da ya samu horo a wajan wani Ba’Amurke mai hada kekuna, da kuma kallon yadda ake koyarwa a yanar gizo.

Ya ce yana so ya zama ya samar da kekuna su zama masu sauki fiye da wadanda su kayi suna. Kekunan da aka sarrafa da itacen gora, wanda akwai su sama da shekaru dari, ya zama hanya mai kyau da za mubi don samun kudaden shiga.