Wani Matashi A Cikin Akwatin Zuwa Turai

Matashi a cikin akwati

Jami’an tsaron kan iyakar kasar Spaniya, a yau talata, sun gano wani matashi dan kasar Gabon, a cikin akwati irin wanda matafiya ke amfani dashi wajan yin bulaguro.

Shi dai wanna matashi mai shekaru goma sha tara, wata mat ace tayi kokarin tsallakawa dashi zuwa kasar Spaniya, ta kan iyakar Ceuta.

Ita dai wanna mata da matashi sun fito daga Morocco ne in ji jami’an tsaron kan iyakar Cueta.

A kwanakin baya jami’an sun tsare wasu ‘yan kasar Morocco biyu, wadanda suka yi kokarin yin sumogal din wasu mutane a cikin akwati domin tsallakawa dasu zuwa cikin kasar Spaniya.