Wani Mai Yiwa Kasa Hidima A Legas Ya Kirkiro Mahajar Kiyaye Haduran Ababen Hawa

LAGOS: MUSA BELLO NA NYSC da ya kirkiro wata mahaja

Wani Musa Bello mai yiwa kasa hidima a Legas ko NYSC a takaice ya kirkiro wata mahajar da zata taimaka wajen kiyaye haduran ababen hawa da kuma ceto rayuka.

Malam Musa Bello wani matashi dake yiwa kasa hidima ko NYSC ya kaddamar da mahajar kiyaye haduran ababen hawa a Najeriya da ma wasu hadura daban daban.

Masana sun ce mahajar zata taimaka gaya wajen kiyaye hadura da ceton rayuka cikin gaggawa a kasar da ta yi kamarin suna a duniya wajen hadura da ababen hawa. Haduran kan haddasa hasarar rayuwa da dukiyoyi na miliyoyin nera kowacce shekara.

Malam Musa Bello a firar da yayi da Muryar Amurka yace ya hada mahajar ce ta buga lambobi da ake kira a takaice da turanci "Emergency Numbers",wato lambobin gaggawa. Yace idan abu ya faru ba sai mutum ya tsaya yana neman yadda zai kira 'yansanda ko ma'aikatan ceton gaggawa ba. Idan mutum nada fasahar cikin wayar hanunsa yana iya kiran masu ceto cikin dan karamin lokaci.

LAGOS: MUSA BELLO na NYSC da ya kirkiro wata mahajar kiyaye haduran motoci

Malam Bello yace idan hadarai ya faru sau tari rashin samun taimakon gaggawa yake kaiga hasarar rayuka.

Shugaban hukumar kiyaye hadura ta Najeritya can baya ya sha nanata kokarin da hukumarsa keyi na rage hadura a hanyoyin kasar.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Wani Mai Yiwa Kasa Hidima A Legas Ya Kirkiro Mahajar Kiyaye Haduran Ababen Hawa - 3' 03"