Rundunar ‘yan sandan jihar Connecticut tace da taimakon wani mai Babur suka sami nasarar cafke wani mai lefi, bayan da mai lefin ya yanka ana kare a ‘kafa.
Rahotanni daga garin Norwich na cewa a ranar Larabar data gabata wasu jami’an ‘yan sanda biyu, suka tare wata mota da ake zargi ta bugawa wata motar kuma mai motar ya arce.
Bayan da ‘yan sanda suka dakatar da motarne kwatsam sai direban motar ya yanka a na kare, hakan yasa jami’an biyu suka bishi da gudu domin su kama shi, suna cikin gudun ne sai ga wani mai Babur yana wucewa da bai san abinda ke faruwa ba, mai babur din dai ya yiwa ‘dan sandan dake bin wanda ake zarga tayin rage masa hanya, haka kuma ya sauke ‘dan sandan gaban mai laifin nan take ‘dan sandan ya makalawa mutumin ankwa.
Duk da yake ba wanda ya san mai Babur din da yayi wannan taimakon, amma ofishin ‘yan sanda sun fityar da wata sanarwar godiya ga mai babur din.
Yanzu haka ana tuhumar direban motar da aka kama da laifukan da suka hada da tuki ba tare da izini ba da laifin mu’amula da miyagun kwayoyi.