Wani mutun da ake zargin cewa mai tabin hankali ne ya kashe mutun daya yakuma ya kuma jiwa mutane ukku, rauni a kauyen Taraya, a karamar hukumar Jahun, dake jihar Jigawa.
Adamu Sani, mazaunin garin wanda kuma akayi a gabansa ya ce shine dai wannan mai tabin hakali yayi amfani da wuka ne wajen tabka wannan ta’asar.
Ya kuma ce wanda ake zargin ya bi mutane har gidajensu ne dake bangarori daban daban na kauyen ya aikata masu wannan aika aika daga bisani kuma ya gudu.
Sakataren karamar hukumar Alhaji Muhammadu Harbo, ya bayyana wa manema labarai cewa shi dai wanda ake zargin ya dabawa Adamu Jibrin, wuka a wuya ne abinda ya yi sanadiyar mutuwar sa, inda shi kuwa Sale Umar a ciki ya daba masa, Auwal Sani, a kafadarsa inda shi kuwa Yusuf Suleman, ya hakarkari aka sauke masa wukar.
Kakakin ‘yan Sandan jihar Abdul Jinjiri, wanda ya tabbatar da labarin yace har yanzu babu wanda aka kama daga ne da laifin.