Wani Likita dan Amurka mai jinyar masu cutar Ebola Shima ya Kamu

Likita Ebola

Wani likita dan kasar Amurka mai jinyar wadanda suka kamu da cutar Ebola a kasar laberiya, shi ma gwaje-gwaje sun nuna ya kamu da kwayar cutar mai kisa.

Dr. Kent Brantly ya na aiki ne da kungiyar agajin jin kai ta Samaritan Purse mai helkwata a nan Amurka, wadda ta ce yanzu haka ya na kwance ya na jinya a wani babban asibitin birnin Monrovia.

A kasar Saliyo kuma jami'an kula da lafiya sun ce wata da ta kamu da cutar Ebola wadda aka yi kokarin farautowa a duk fadin kasar bayan da dangin ta suka dauke ta daga asibiti da karfi, su ka kai ta wurin wani mai maganin gargajiya, ta mutu a cikin motar daukan marasa lafiya a kan hanyar maida ita asibiti.

Jami'an kula da lafiya sun ce a kasar Saliyo mutane na kawo cikas wajen dakile yaduwar cutar saboda da yawan su sun fi amincewa da maganin gargajiya don wasu dalilai masu nasaba da tsoro da kuma rashin yarda da masu aikin jinya a asibiti