Wani Kwararre A Harkar Tsaro Ya Yaba Da Taron Tsaro Na Yankin Tafkin Chadi

  • Ibrahim Garba

Shugaban Najeriya a wurin taron tsaro na yankin tafkin Chadi

A cigaba da bayyana ra'ayoyi da ake yi kan taron tsaro na yankin tafkin Chadi, wani kwararre ya ba da shawarar a rinka taron kowace shekara.

Wani kwararre a fannin tsaro, Manjo Yahaya Shinku y ace ganin muhimmancin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan Tafkin Chadi, ya kamata a ce ana gudanar da taron Tafkin Chadi kowace shekara ta yadda za a rika karba-karba tsakanin kasashen ko kuma ta wata hanaya daban.

Da ya ke zantawa da wakiliyarmu a Abuja Madina Dauda, Manjo Shinku ya ce tsaron rayuka da dukiyar jama’a babban abu ne don haka ya kamata a ba da himma sosai kan batun tabbatar da tsaro.

Manjo Shinku ya ce mai yiwuwa a baya kasashen Amurka da Faransa sun ki taimaka ma kasashen da ke yaki da Boko Haram din ne saboda sun a shakkar niyyar kasashen da ke yaki da ‘yan bindigar. Y ace kasashen na Yamma na sane da irin rashin gaskiyar da kasashen da ke yaki da Boko Haram ke fama da shi musamman ma Najeriya, inda aka bankado almundahanar da aka yin a kadaden yaki da Boko Haram.

Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Wani Kwararre A Harkar Tsaro Ya Yaba Da Taron Tsaro Na Yankin Chadi- 3'5''