WASHINGTON DC, —
Wani Kwale kwale ya kife a wani kogi a yakin Bengaji dake karamar hukumar Yabo dake jahar Sokoto wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane mutane shida.
Kakakin karamar hukumar ta Yabo, Alhaji Mika'ilu Sabo Yabo,ya ce Kwale Kwalen ya rabe biyu ne a lokacin da yake tsakar tafiya a kogin Bengaji, ya kara da cewa mutanen da suka mutu sun fito ne daga kauyukan Kissa, Gadara da Kalangu.
Mutane hudu daga cikin wadanda ke cikin Kwale Kwalen sun samu sun tsira da rayukansu.
Shugaban karamar hukumar Alhaji Ahmad Shehu, bayan da ya yiwa iyalen mamatan ta'aziya ya ce bincike zai bayana musabbabin afkuwar hatsari.