Da safiyar yau juma’a an tsinto wasu gawarwaki hudu sannan an ceto wasu bakin haure 342 a wani kwale kwale da ya nutse a tekun mediteraniya, a cewar kungiyar da ke sa ido kan halin da bakin haure ke ciki.
WASHINGTON D.C —
An yi kiyasin cewa mutane 700 ne suke cikin kwale-kwalen na katako wanda ya nutse da sanyin safiyar yau.
Kakakin kungiyar da ke kula da bakin haure a Girka, ta gayawa Muryar Amurka cewa da safiyar yau ne wani kwalekwale mai tsawon mita 25 ya aike da sakon neman agajin gaggawa.
Yanzu akalla jiragen ruwa biyar da jirgi mai saukar ungulu suna can suna cigaba da neman sauran wadanda hadarin ya rutsa da su.
Ya zuwa yanzu kuma ba a tantance daga inda bakin hauren suka fito ba, sannan makomarsu za ta dogara ne da ko su ‘yan gudun hijra ne.
Kuma duk wanda aka gane bakin haure ne, akwai yiwuwar a maida shi kasarsa muddin ba ya cikin ‘yan gudun hijra.