Wani Jirgin Saman NATO Ya Kusanci Wani Jirgin Saman Rasha Dake Dauke Da Wani Kusa

Russia NATO

Kamfanin dillancin labarai na kasar Rasha ya ruwaito cewa wani jirgin saman NATO, ya kusanci wani karamin jirgin saman Rasha dake dauke da Ministan tsaron kasar Sergie Shoigu a yau Laraba, yayin da yake shawagi a daidai tekun Baltic, amma kuma daga karshe aka mai rakiya ya fice daga yankin.

Rahotanni sun ce jirgin na NATO ya kusanci jirgin da ministan ke ciki ne yayin da yake tafiya a yankin ruwan da ba mallakar kowa ba.

Daga baya kuma wani jirgin Rasha ya shiga tsakanin jiragen Ministan da na NATO, ya yi barazana, inda ya jujjuya jikinsa domin ya nuna cewa yana dauke da makamai.

Bayan haka sai jirgin NATOn ya fice daga yankin yayin da shi kuma jirgin Rashan ya samu daidaito.

Ita dai rundanar tsaro ta NATO ta ce abinda da jrgin yakinta ya yi abu ne da ta saba yi a matsayin matakin tabbatar da tsaro.

Wani babban jami’i a rundunar tsaron ta NATO ya fadawa Muryar Amurka cewa, a ‘yan kwanaki nan ana samun yawaitar shawagin jiragen Rasha a yankin na tekun Baltic, kuma ba sabon abu bane NATO ta dauki matakin bibiyar duk wani jirgin dake bin yankin tekun na Baltic.