Wani Hatsarin Jirgin Ruwa A Jihar Sokoto Ya Yi Sanadin Asarar Rayuka Da Bacewar Wasu Da Dama

Boat accident in Sokoto State

Ana ci gaba da aikin ceto rayukan wasu 'yan Najeriya da akalla ba zasu rasa kai goma sha uku ba a wani hadarin jirgin ruwa da ya auku jiya Lahadi a Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya.

Jirgin kwalekwale ne na katako dauke da mutane fiye da 35 ya nutse, inda kawo yanzu ake aikin lalabo gawarwakin wadanda suka mutu cikin ruwan.

Hadarin ya auku ne agarin Dundaye na karamar hukumar Wamakko a jiahr Sakkwato a cikin gulbin Rima wanda ke dauko ruwa daga madatsun ruwa na Bakalori ta jihar Zamfara da Goronyo ta jihar Sakkwato.

Mutanen da suka hada da manya da yara, maza da mata sun shiga kwalekwale a tsallaka ruwan da su, su je aiki cikin fadama.

Boat accident in Sokoto

Muhammad Bello wani dattijo ne wanda gaban sa lamarin ya faru, ya ce jirgin ya dauki mutane fiye da kima kuma sai da mai tukin jirgin ya so mutane su rage suka ki.

Bayan ya tashi ya hau ruwa yana kai tsakiya sai ya soma kwasar ruwa daga nan sai ya nutse, amma dai a cewar sa an samu ceto wasu da rayuwa.

Wakilin Sarkin Adar na Dundaye Muhammad Bello Hassan yana daga cikin muhimman mutane da suka fara zuwa wurin bayan samun labarin nutsewar jirgin, ya ce mafi yawan wadanda abin ya rutsa da su zasu je ne wurin yin kayan wuta da kuma aikin kalar shinkafa.

Sokoto boat accident

Sa'idu Dundaye na daga cikin wadanda suka samu tsira da rayuwa a cikin wannan hatsarin, amma ya ce shi ma da kyar ya sha kafin ya samu fita daga cikin ruwan.

Tuni da jami'an gwamnatin Sakkwato karkashin jagorancin mataimakin gwamna Idris Muhammad Gobir suka ziyarci wurin tare da Jami'an hukumar bayar da agajin gaugawa ta kasa domin ganin yadda lamarin yake, kuma Muryar Amurka ta zanta da shugaban hukamar kula da bayar da agajin gaugawa ta Najeriya mai kula da shiyar Sakkwato Aliyu Shehu Kafin Dangi.

Ya ce “an samu ceto kimanin mutane 19, aka samu gawar mutum daya kuma ana kan neman mutune goma sha uku zuwa sha hudu.”

Sokoto boat accident

A cewar sa ana amfani da masu nutsu cikin ruwa wurin lalabo sauran mutanen da suka makale, kuma an bayar da rahoto a wasu wurare da ake sa ran ruwa zasu iya jan mutanen sukai su can domin su kula koda ruwa sun kai gawarwakin sauran mutanen can.

Wannan dai shi ne hadarin kwalekwale na hudu da ya faru a jihohin Najeriya hudu kasa ga mako daya, domin an samu kwalekwale da ya kama da wuta a jihar Bayelsa, sai hadarin kwalekwale a jihohin Jigawa da Zamfara, yanzu kuma ga wannan a Sakkwato, abinda ke nuna akwai bukatar a yi wani abu don kaucewa irin wannan matsalar wadda ta yi ta salwantar da rayukan jama'a.

Ga rahoton Muhammad Nasir daga Sokoto cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Wani Hatsarin Jirgin Ruwa A Jihar Sokoto Ya Yi Sanadin Asarar Rayuka Da Bacewar Wasu Da Dama.mp3