WASHINGTON D C —
Wata babbar fashewar bom ta ratattaka wata kasuwa da safiyar yau Jumma’a a kudu maso yammacin Pakistan, akalla mutane 18 sun rasa rayukan su wasu su 48 kuma sun jikkata.
Jami’an ‘yan sandan kasar sun ce wani bom da aka dana a wani shago ne ya haddasa fashewar a yankin Quetta babban birnin lardin Baluchistan wanda galibin sa ‘yan Shi’a ke zama ko suke hada-hadar kasuwancin su, haka kuma wasu daga cikin tsirarun kabilun yankin na cikin wadanda harin ya shafa.
“An kaddamar da bincike akan harin don gano dalilin sa,” a cewar Abdul Razzaq Cheema, mataimakin Supeto Janar din ‘yan sandan kasar.
Nan take dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin da ya faru a wurin kasuwar Hazarganji da dama a baya an sha kai mata hari.