Wani Hari Ya Kashe Wasu Yan Taliban a Afghanistan

Herat Civilian Casualties

Mukaddashin Ministan tsaron Afghanistan ya ce, nan ba da jimawa ba, gwamnatinsu za ta gabatar da hujjoji da ke nuna cewa wani harin sama da aka kai a Lardin Herat da al’ummar yankin suka ce ya kaikaici wani wajen bikin aure, ya kashe wasu mayakan Taliban.

A yau Alhamis Asadullah Khalid ya fadawa wani taro a Kabul cewa, ma’aikatarsa ta na da bidiyon harin wanda aka kai a jiya Laraba a Gundumar da ake kira Adraskan, wanda ya tabbatar da cewa akwai mayakan Taliban a harin na kauyen Khom-e Zairat.

Ya kuma ya yi fatan ganin an gudanar da bincike, wanda zai tabbatar da cewa ba bu wani farar hula da harin ya rutsa da shi.

Ma’aikatar tsaron ta nemi a gudanar da binciken ne bayan da al’umar yankin suka yi ikarin cewa an kashe fararen hula takwas a harin, kana an jikkata wasu da dama ciki har da kananan yara a harin wanda dakarun Afghanistan suka kai da safe.

Kakakin gwammnatin Lardin na Heratt, Jailani Farhad ya ce gomman mayakan Taliban suna wajen bikin a lokacin da aka kai harin.