Sojojin Amurka sun ce sun kai hari ta sama a yankin Puntland na Somaliya wanda ya kashe mutane bakwai wadanda ke mara wa mayakan kungiyar IS baya.
Sashen Somali na Muryar Amurka, da farko ya ba da rahoton kai harin a ranar Talata 21 ga watan Yuli. Jami'an yankin da shaidun gani da ido sun shaida wa Muryar Amurka cewa, sojojin yankin Puntland sun yi wani samame a kan 'yan bindigar a Turmasale da Amayra, wuraren da suke da tsaunuka a kusa da kauyen Timirshe, mai tazarar kilomita 140 a kudu maso gabashin Bosaso.
A wata sanarwa a jiya Laraba daga rundunar sojojin Amurka da ke Afirka, sun ce an kai harin ta sama ne a yayin wani hari da sojojin kawancen suka kai.
"Muna ci gaba da matsin lamba kan kungiyoyin 'yan ta'adda tare da taimaka wa abokan aikinmu na Somaliya wajen dakile ayyukansu," a cewar kakakin rundunar sojin Amurka Brigadier Janar Miguel Castellanos, kuma mataimakin darektan ayyukan AFRICOM. Ya kuma ce "muna ci gaba da goyan bayan Somalia don kawar da kungiyoyi irin su ISIS da al-Shabaab."