Wani Farmaki Ta Sama A Somalia Ya Ya Shafi Sansanin 'Yan ISIS

Wani hari ta sama da ake kyautata zaton Amurka ce ta kai shi ya taba wani sansanin mayakan ISIS a yankin Puntland dake kasar Somalia, a cewar mazaunan yankin.

Wani wanda ya shaida lamarin, da yayi magana da Muryar Amurka bisa sharadin a sakaya sunansa, ya ce kusan makamai masu linzame 4 da wasu jiragen sama marasa matuki suka harba, wadanda ake kyautata zaton na Amurka ne sun dira kan wani yanki mai tsaunuka a jiya Jumma’a a kusa da kauyen Ameyra, mai tazarar kilomita 150 kudu da birnin Bosaso.

Jami’an tsaron Puntland da Muryar Amurka ta tuntuba sun ce sun sami labarin harin amma ba su ce komai ba akan batun saboda suna kan gudanar da bincike da kuma tattara bayanai.

Wani hari da aka kai a watan Afirilu ya kashe mataimakin shugaban kungiyar ISIS na Somalia, Abdulhakim Dhuqub, wanda shi ke da alhakin kula da harkokin kungiyar a ko da yaushe kafin mutuwarsa.