A wani al'amari da hukumomi ke fassarawa da aikin ta'addanci, wani matashi ya kashe mutane biyu daga cikin wadanda ya yi garkuwa da su kafin daga baya jami'an tsaro su ka zagaye babbar kasuwar zamanin da ya yi garkuwa da mutane.
WASHINGTON D.C. —
Ma’aikatar Cikin Gidan Faransa ta fadi yau Jumma’a cewa an kashe mutane akalla biyu bayan da wani dan bindiga, wanda aka ce ya yi shelar mubaya’a ga kungiyar ‘yan bindiga ta ISIS, ya bude wuta a wata babbar kasuwar zamani, inda ya yi garkuwa da mutane a garin Trebes da ke Kudu maso Yammacin Faransa.
‘Yansandan kasa sun ce jami’an tsaro sun yi kawanya ma maharin a wannan babbar kasuwa, kuma da yiwuwar an yi garkuwa da mutane.
Firaminista Edouard Philippe ya ce masu bincike na daukar wannan al’amarin a matsayin aikin ta’addanci.
Ofishin babban lauyan gwamnati da ke Paris ya ce hukumomin da ke yaki da ta’addanci sun karbi aikin binciken to amma bai yi karin bayani ba.