Wani Dan Sama Jannatin Amurka Ya Shiga Littafin Tarihi

Daya daga cikin Amurkawa yan sama jannati da wasu yan Rasha biyu sun sauko lamin lafiya a Kazakhstan da safiyar Laraba bayan da suka kwashe watanni shida suna gudanar da ayyuka a sararin samaniya.

Dan sama jannatin nan da ga Amurkan Jeff Williams, ya kafa tarihi a Amurka wanda ya zama na farko da yafi kowa dadewa a duniyar Orbit, wanda ya kai shi ga yin kwanaki 534 a sararin samaniya a ayyuka dabam-dabam hudu. Wani dan sama jannati Scott Kelly shine ke da tarihin baya a Hukumar sama jannati da harkokin sararin samaniya ta Amurka NASA inda yayi kwanaki 520 a sararin samaniya. Wani dan Rasha ne ke rike da babban tarihin sama jannati na duniya inda yayi kwanaki 879 a sararin samaniya.

Williams tare da wasu yan Rasha da suka hada da Alexy Ovchinin da Oleg Skripochka sun sauka da jirgin shiga sararin samaniyar kirar Rasha a tsakiyar Kazakhstan da karfe 7 na safiyar Laraba ijin hukumar NASA. Mutane ukun sun dauki kimanin awa uku da rabi kafin su bar wurin saukar jirgin a cikin samaniya bayan sun sauka.

A wata sanarwa da NASA ta fitar, ta kira Williams kokarta wurin ya shirywa ma’aikatar jiragen shiga samaniyar yan kasuwa na Amurka da zasu isa wurin a wata rana. Sanarwan tace Williams ya zaga sau biyar a lokacin da ya isa samaniya, wanda a cikin dayan zagayen ya kafa na’urar da zata ba jiragen kasuwanci na Amurka daman sauka wurin.

Bayan Williams ya bar tashar ne said an Rasha Anatoly Ivanishi ya dau ragama. Ya kuma kasance da yar Amurka Kate Rubins da dan Japan Takuya Onishi

Williams ya dora akan shafinsa na Twittera ranar Talata, inda yake cewa zai yi kewar wannan wuri tare da wasu hotuna da ya dauka a wurin. Ya kuma mkia dubun godiya ga ma’aikatar jirginsa da kuma taimakon danginsa da abokan ariziki