Rahotanni sun ce wani dan kunar bakin wake ya hallaka a kalla mutane 4 a wani shahararren gidan cin abinci da jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati ke zuwa sosai a Mogadishu.
WASHINGTON D.C. —
Wasu mutane da dama sun samu raunuka a wurin cin abincin na Lul Yamani dake tsakiyar Mogadishu, babban birnin Somali.
'Yan sanda sun bayyana cewa dan kunar bakin waken ya tayar da bomb din dake jikin shi ne bayan da mai tsaron gidan abincin ya hana shi shiga.
Duk da cewa babu wanda ya dau alhakin kai harin, ana zargin mayakan Al-shabab da kai harin saboda tarihinsu na kai hari kan jami’an tsaro.