Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ko OTAN, ta ce wani mutum cikin kakin sojojin kasar Afghanistan ya bude wuta kan sojojin taron dangi, ya kashe daya a cikin su.
A cikin sanarwar da NATO ta gabatar, ta ce sojojin taron dangin sun maida martani kan mutumin da ya bude mu su wuta a yau Lahadi a kudancin kasar Afghanistan.
Wannan harbi shi ne na baya-baya a cikin jerin munanan hare-haren da ‘yan bindiga sanye da kakin sojojin Afghanistan, ke kaiwa sojojin taron dangin kasa da kasa.
A wani tashin hankali na daban kuma, NATO ta ce sojin ta daya ya mutu a cikin fashewar bomb a yau Lahadi a gabashin kasar Afghanistan, daga nan ba ta yi wani bayani dalla-dalla ba game da harin.
A wani bangaren kasar kuma, an kashe wasu kwamandojin ‘yan Taliban biyu da ‘yan tawaye uku cikin fadan da aka fafata ranar Jumma’a da jami’an tsaro. A cikin wata sanarwar da ta gabatar, NATO ta ce daya daga cikin wadanda aka kashen, babban kwamandan ‘yan Taliban ne mai shirya hare-haren boma-boman gefen hanya da kuma tsara sauran hare-haren da ake kaiwa sojojin Afghanistan da na taron dangin kasa da kasa a duk fadin lardin Faryab.
Gudan kuma mataimakin kwamanda ne, kuma alkalin ‘yan Taliban wanda ya yi kokarin tilasta dokoki da hukuncin ‘yan Taliban akan fararen hular yankin.