Wani Beran-Masar ya yi batan hanya, inda ya kasa maida kansa gida. Wani mutum da ya tsinci beran a tsakiyar titi a birnin Vermont ya mika shi ga hukumar 'yan sanda na yankin don adana shi.
Wani mutum da yake tafiya a kasa ne ya tsince beran a kusa da titin layin dogo, kamar yadda jami’in ‘yan sanda Kofural George Johnson ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Caledonian.
Wani ma'aikacin kashe gobara Phil Hawthorne ya ce idan babu mai shi za su ci gaba da rike beran, don ya zama abokin aikin su a ma’aikatar ta ‘yan kwana-kwana. Shi kuwa wani mutum ya bada tashi gudunmawar abinci da keji ga beran.
'Yan sanda sun sanar da cewa duk mai wannan beran masar din ya je gidan kashe gobara da ke kan titin Main don tabbatar da mallakar dabbar kamin a bashi.