Wani Bam da Ya Fashe a Mogadishu Yayi Sanadiyar Mutuwar Akalla Mutane 10

Wani sojan Somali na duba wurin da bam ya tarwatse

Kungiyar al-Shabab ta tayar da wani bam a birnin Mogadishu wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla goma

A kalla mutane 10 ne suka mutu biyo bayan fashewar wata mota shake bom a babban birnin Mogadishu dake Samaliya.

Wasu mutane 15 ne suka samu raunuka daura da wani sanannen Otel da wajen shakatawa Lahadinnan dake kan hanyar garin Maka al Mukarama.

Jami’ai sun dora alhakin fashewar akan mayakan al-Shabab, wadanda suka yi kaurin suna wajen tayar da boma-bomai da kai hare-haren bindiga a Mogadishu.

A baya-bayannan, wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su waye ba, sun kai hari akan wani dan jarida mai zaman kanshi a Mogadishu inda ma yaji raunuka.

Wannan dan jarida mai suna Abdirisak Jama Elmi wanda aka fi sani da inkiya “Black” ya samu raunuka ne bayan harbinsa sau dayawa da aka yi a kofar gidanshi dake yankin Howlwadag a lokacin da yake kan komawa daga wajen aiki. Ofishin kungiyar tarayyar Afirka dake Samaliya tayi Allah wadai da harin, wanda shine karo na 3 da aka kaiwa ‘yan jaridu a Samaliya duk a cikin wannan shekara.