Wani Al'amarin Soyayya Ya Bayyana A Taswirar Google

Taswirar Google

Wani matashi dan kasar Jamus mai suna Steffen Schwarz dan shekaru 32 da haihuwa, ya kafa tarihi a duniyar soyayyar. Matashin wanda yake son ya bayyana wa masoyiyarsa yana so ya aure ta, ya tsara rubutun tayin neman aure wanda ya ce "za ki aure ni?" da shukar masara a gonar sa.

Na'urar daukar hoton taswira da matafiya ke amfani da ita mallakar kamfanin Google ce ta bayyana hoton daga sama.

Kamfanin dillacin labarai na Jamus na DPA ya bayyana cewa Steffen ya yi amfani da wani inji ne don yin shukar ta yadda rubutun ya fito sosai.

Schwarz ya ce ya gayyaci budurwar da ta yi amfani da jirgin sama mai sarrafa kansa da ake kira Drone, don yin shawagi a sararrin saman gonarsa a watan Mayun bara a Huettenberg dake tsakiyar Jamus. Kuma budurwar ta amince da tayin.

Schwarz ya kuma shaidawa kamfanin dillancin labaran cewa ba da niyar rubutun ya bayyana a taswirar Google ya yi shukar soyayyar ba, amma wata Gwaggon sa dake kasar Canada ce ta ja hankalin sa akan shukar.