Tsohon dan wasan kwallon kafa na Kasar Brazil Kaka, ya bada sanarwar ajiye takalmam taka leda a bangare kwallon kafa gaba daya,
Kaka, mai shekaru 35, da haihuwa ya fara buga wasan kwallon kafa ne a shekarar 1994, kimanin shekaru 23 da suka gabata a wata kungiyar kwallon kafa ta matasa mai suna Sao Poulo dake kasar Brazil.
Kaka, ya buga wasanni a manya-manyan kungiyoyin kwallon kafa daban daban na duniya Irinsu AC Milan, ta kasar Itali, da kuma Real Madrid, ta Spain.
Haka kuma yana daga cikin jerin fitattun ‘yan wasa takwas da suka lashe manyan kofuna da yawa a lokacin suna murza leda, irinsu Bobby Charlton, Gerd Muller, Beckenbauae, Paolo Rossi, Zinedine Zidane, Rivaldo, da kuma Ronaldinho.
Kaka ya lashe kofuna kamar haka Confederations Cup, World Cup, UCL, Serie A, na kasar Itali, sauran kofunan sun hada da Supercoppa Italiana, da UEFA Super Cup, Club World Cup, Laliga da Copa del Rey na kasar Spain,
Kaka ya fafata wasani har guda 46, a kungiyoyi daban daban, ya kuma samu nasarar jefa kwallaye 149, a raga.
Kaka ya taba zamowa gwarzon dan wasan duniya a shekarar 2007 haka kuma ya zamo dan wasa mafi tsada a duniyar kwallon kafa a shekara 2009 inda Real Madrid, ta saye shi a kudi Fam miliyan £56 daga kungiyar kwallon kafa ta AC Milan.
Daga karshe Kaka, ya kammala kwallon sa ne a wannan shekara ta 2017 a kungiyar Sao Poulo, ta Kasar Brazil, a matsayin aro daga kungiyar Orlando City.
Your browser doesn’t support HTML5