Tawagar ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya mai zuwa wajan babban zaben hukumar kwallon kafa FIFA karo na 65, a garin Zurich zata kasan ce ne a karkashin jagorancin shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya NFF a takaice Amaju Pinnick.
Za a gudanar da zaben ‘yan majalisar hukumar FIFA ne a shalkwatar hukumar da ke Zurich, kasar Switzerland inda za’a ga shugaban kungiyar kwallon kafa ta Jodan yarima Ali bin al-Hussin zai kalubalanci shugaban kungiyar mai ci yanzu Sepp Blatter.
A halin yanzu an riga anyi waje da Dutchman Van Praag da tsohon kyaftin din Potugal Luis Figo daga fafatawar.
Mataimakin hukumar kwallon kafar ta Najeriya na farko Barrister Seyi Akinwumi da babban sakataren kungiyar Dr Mohammed Sanusi, na cikin wadanda za su mara wa shugaba Pinnick baya.
Babban mai kujera na fannin lafiya akan harkokin wassanni Dr Abdulkadir Mu’azu, shima zai halacci taron fannin lafiya a gefen taron majalisar ta FIFA.
Kuma ana sa ran shugabannin hukumar ta Najeriya za su koma gida cikin karshen wannan satin.