Wakilan Majalisar Wakilai Ta Najeriya Sunyi Wani Zama Na Gaggawa Kan Cire Tallafin Mai

Masun zanga-zanga kan cire tallafin mai a Legas.

Wakilan majalisar wakilai ta tarayya a Najeriya tayi kira ga gwamnati ta warware shawarar da ta tsayar na janye tallafin mai, mataki da ninka farashinmai ya kuma janyo zanga-zanga a duk fadin kasar cikin makon jiya.

A wani zaman gaggawa da wakilan sukayi lahadin nan, sun kada kuri’ar wani kuduri da yayi kira ga gwamnati ta maido da tallafin mai wadda gwamnatin take kashe fiyeda dala milyan dubu takwas.

Tashin farashin mai ya janyo tashin gorron zabbi kan farashin kayan abinci, sufuri, da sauransu.

Manyan kungiyoyin kwadago biyu na kasar sun ayyana fara yajin aiki daga ranar litinin tara ga wata.

Najeriya tana da arzikin mai, amma ta dogara ne kan mai da ake shigowa dashi daga ketare, domin matatun man ta duk sun tsaya sabo shekaru da aka yi ba a kulawa da su.

Aika Sharhinka