Wakilan Kasashe Fiyeda 70 Sun Hallara Domin Taro Kan Rikicin Syria

A wan nan hoto Sarki Abdullah na Saudiyya ne daga hanun dama yake ganawa da sakatariyar harkoki wajen Amurka Hillary Clinton.

A wan nan hoto Sarki Abdullah na Saudiyya ne daga hanun dama yake ganawa da sakatariyar harkoki wajen Amurka Hillary Clinton.

Fiyeda ministocin harkoin waje na kasashe 70 na yammacin duniya da na larabawa suke hallara yanzu haka a Istanbul yau lahadi domin kara matsin lamba kan Damascus ta aiwatarda shirin tsagaita wuta.

Fiyeda ministocin harkoin waje na kasashe 70 na yammacin duniya da na larabawa suke hallara yanzu haka a Istanbul yau lahadi domin kara matsin lamba kan Damascus ta aiwatarda shirin tsagaita wuta bat area wani bata lokaci ba, da kuma kira ga ‘yan hamayya su hada kai a yanzu yake warwatse.

sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da wasu jami’ai da zasu halarci taron na “kawayen Syria” zasu dage cewa tilas shugaba Assad ya aiwatarda daftarin zaman lafiya da manzo na musamman da majalisar dinkin duniya da kungiyar kasashen larabawa suka nada, watau kofi Annan ya gabatar.

Shugaba Assad, wanda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana cewa an murkushe boren kasar, yace ya amince da sharudda shida nan da Kofi Annan ya gabatar. Amma kasashen yammcin duniya da na larabawa duka suna nuna shakku kan furucin nasa ganin har yanzu ana gwabza fada.