Waka Kusan Gado Ce A Wuri Na -In Ji Messie

Yahaya Birgade Messie

Wakar kusan kamar gado ne a wuri na in ji Yahaya Birgade, wanda aka fi sani da Messien mawaka ya furta haka ne a wata hira da suka yi da dandalinvoa.

Ya ce yana waka ne domin ya fadakar ya kuma nishadantar da al’uma, a cewarsa dalilin da yasa ya ce waka kamar kusan gado ne wajensa shine domin mawaki Haruna Oji aminin mahaifinsa ne baban, wanda ha kan ne ya sa ya lakanci waka.

Yana mai cewa ya na isar da sakonnin ta kowanni fanni inda yake aika sakwaninsa ta nishadi da kuma wakokin siyasa, yace burinsa ayyi fice a fagen waka a duniya.

A fannin mu na tsegumi kuwa wani masoyin fitaccen mawakin nan Ycee, ya tambaye shi ta kafar sadarwa ta Twitter, da ya bashi wayar iPhone, mawakin da aka fi sani omo Alhaji dai ya mayar wa masoyin nasa martini da cewar ya tambayi kamfanin Apple da ya bashi wayar

Your browser doesn’t support HTML5

Waka Kusan Gado Ne In Ji Messie - 5'39"