Fitaccen mawakin Hausan nan na zamani da ya shahara a fannin wakokin hip hop, Haruna Abdullahi wanda aka fi sani da DJ AB ya ce waka ta taimaka mai matuka wajen koyon yadda zai sarrafa harshen turanci.
Matashin mawakin, ya ce lokacin da ya fara waka, ba ya rabuwa da kamus a kullum saboda rashin kwarewarsa sosai a harshen.
Wannan lamarin zai zo wa mutane da dama da mamaki, ganin yadda mawakin ya yi suna bisa wakokin gambara da yake yi inda yake hada kalmomin Hausa da na turanci.
A cewar mawakin wanda ya rera wakar ‘totally,’ “lokacin da na fara waka ban iya turanci sosai ba, bisa haka a lokacin sai ina yawan bude kamus domin binciko kalmomin da zan rinka amfani da su.”
“Waka ta taimake ni sosai, saboda ta kara min sanin abubuwa.”
Haruna Abdullahi wanda dan arewacin Najeriya ne yakan sha yabo duba da yadda yake sarrafa harshen idan yana magana da turanci.
Amma a cewar matashin, ba haifarsa aka yi da kowacce baiwa ba, dagewar da ya yi ne da kuma mayar da kamus abokin huldarsa ta yau da kullum ya kawo shi inda yake yanzu.
Mawakin dan jihar Kaduna, wanda yake kokarin kammala jami’a ya ce ya fara harkar wake-wake ne tun yana makarantar sakandare, inda ya zuwa yanzu ya yi waka akalla 1000.
Ya jaddada yadda shi da abokan aikinsa suka sha wahala kafin su samu karbuwa daga mutane, abin da ya alakanta da yanayin “al’adar Hausa”.
Mutane na yawan yi wa wadanda ke shiga harkar wake-wake ko kuma fina-finai a arewacin Najeriya kallon kamar suna yin abu marasa kyau.
Sai dai masana wannan fannin sun sha karyata wannan ikrarin.
Shi ma Haruna Abdullahi ya bi sahunsu inda ya ce “na san abin da nake yi ba abu mara kyau ba ne, saboda haka Allah kadai zai iya yi min hisabi.”
Dangane da hakan ne matashin ya ce ya zabi bin sahun yin wakar zamani ta hip hop, duk da cewar ba kasafai aka saba samun masu bin wannan fannin na waka a Arewacin Najeriyar ba.
“Yin wakar gambara yana bani damar fadan abubuwa masu ma’ana, sabanin yadda ba a cika samun damar yin hakan ba a wakokin da ba na gambara ba,” in ji DJ AB.
A cewarsa, yana son amfani da damar da yake da ita ta yin waka domin fadakar da matasa kan abubuwan rayuwa.
Ko a 'yan kwanakin nan ma, Haruna Abdullahi da kaninsa Abdulhafiz Abdullahi (Feezy) sun rera wata waka wacce ta mayar da hankali wajen fadakar da matasa, da kuma kara janyo hankulansu wajen bin matakan da hukumomin kiwon lafiya suka jaddada cewa a bi domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.
WASHINGTON D.C. —