Wajen Mutane Miliyan 100 Ne Zasu Kalli Muhawarar Hillary Da Donald

Shirye shiryen muhawara da za a yi tsakanin Hillary da Donald

An yi kiyasin cewa mutane wajen miliyan 100 ne za su kalli muhawarar da za a yi tsakanin 'yar takarar Shugabar kasa karkashin jam'iyyar Democrat Hillary Clinton da na Republican Donald Trump; lokacin da wadanda su ka kalla za su iya alkalanci kan 'yan takarar a karon farko, lokacin da su ke tsaye a wuri guda.

Duka 'yan takarar biyu na fuskantar kalubale mai girma. Ba game da abubuwan da 'yan takarar su ke fadi ne kawai 'yan kallon za su mai da hankali ba, har ma da yadda su ke maganar da kuma yadda su ke mai da martani ga juna.

Muhawarar za ta kasance wata muhimmiyar dama ga Trump, wanda ya cimma Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat a akasarin kuri'un jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan, musamman saboda ya nuna natsuwa fiye da yadda ya nuna a baya. Ya kuma mai da hankali kan sakonninsa.

A tana bangaren kuma, Clinton za ta iya amfani da muhawarar wajen sake bayar da kwarin gwiwa ga magoya bayanta, ta kuma kara jaddada alkawarinta na gina tattalin arziki mai alfanu ga kowa, kamar yadda ta yi a wani gangami na bayabayan nan a Orlando, jahar Florida.