Wai Shin Mene Ne E-Naira (Tsarin Kudi Na Lataroni)? Mene Ne Alfanunsa?

  • Ibrahim Garba

Ibrahim K Garba

Kamar sauran 'yan Najeriya da dama, Hajiya Zainab Matar Hussaini Ali Maigishiri Rijau ta na son a ma ta bayani game da tsarin kudi na yanar intanet wanda ake tafi da shi ta kafar lataroni (digital).

Ga cikakkaiyar tambayar Malama Zainab:

Assalama alaikum Sashin Hausa. Ina so ku yi mani Karin bayani akan sabon kudin Intanet wato E-Naira, wanda gwamnatin Najeriya ta kaddamar a ranar Litini 25 ga watan 10 na wannan shekara ta 2021. Ko wani alfanu wannan tsarin kudi ya ke da shi ga tattalin arzikin Najeriya? Kuma ta yaya mu mazauna karkara za mu iya yin amfani da wannan kudi na E-Naira? Sannan wani tabbaci ake da shi cewa ‘yan damfara a yanar gizo, ko sauran ‘yan damfara, ba za su cuci masu amfani da wannan tsarin kudi ba?

Mai tambaya Zainab Matar Hussaini Ali Maigishiri Rijau.

To idan Malama Zainab na saurare, ga amsar da wakilinmu a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, ya samo maki daga Dr. Lawan Habib Yahaya na Sashin Koyon Harkokin Banki da Kudi a Kwalejin Kimiyya Da Fasaha ta jihar Kano, Kuma tsohon Mukaddashin Shugaban Kwalejin. Sai a gyara zama a saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

Wai Shin Mene Ne Tsarin Kudi Na E-Naira? Mene Ne Alfanunsa?