Sakamakon jarabawar ya nuna cewa daga cikin yara miliyan daya da rabi da suka rubuta jarabawar a duka fadin Najeriya kimanin dalibai 616,000 ne basu samu cin akalla fannoni biyar ba.
Hukumar ta rike sakamakon jarabawar na dalibai 118,000 wadanda ta zarga da yin magudi banda na jihohi 13 da ta rike saboda bashin da take bin gwamnatocinsu.
Kodayake hukumar bata bayyana sunayensu ba amma bincike ya nuwa cewa yawancin jihohin suna arewacin kasar ne yankin da tun ba yau ba yake kuka kan koma baya na fuskar ilimin boko.
A cewar shugaban hukumar ta WAEC Mr. Charles Ikwedu tuni wasu jihohi suka fara tuntubarsa saboda ganin cewa an saki sakamakon jarabawar daliban. To saidai yace wannan ba lokaci ba ne na roko lokaci ne na biyan kudi domin ita hukumar ta samu sakunin sauke wasu nauyi dake kanta kamar biyan albashi da alawus alawus na masu gudanar da jarabawa da kuma harkoki na yau da kullum..
Daga yankin arewacin Najeriyan wasu sun fara bayyana yadda suka ji da rike sakamakon jarabawar. Wani yace basu ji dadin abun da ya faru ba. Abun kunya ne a ce daidai lokacin da duniya ke ci gaba da karatun boko matasan arewa ana barinsu baya saboda rike sakamakon jarabawarsu. Shugabannin arewa basu damu da ilimin matasa ba. Basu bar iyaye suna biyan kudaden jarabawa ba su kuma basu biya ba.
Iyaye ma sun bayyana rashin jin dadinsu da rike sakamakon jarabawar 'ya'yansu amma kuma sun dora laifin kan gwamnatocinsu da suke yin alkawari ba tare da cikawa ba.
Ga cikakken rahoton Babangida Jibril.
Your browser doesn’t support HTML5