Masu iya Magana sun ce “abincin wani gubar wani”, wannan Magana haka take domin kuwa ga dukkan alamu daukacin ‘yan adam na da ra’ayoyi mabambanta akan harkokin da suka shafi zamantakewa, soyayya, zaman aure da sauran su.
Wasu daga cikin dalilan wannan batutuwa sune ra’ayoyin da shirin samartaka na dandalinvoa ya samu daga dimbin matasa akan tambayar da shirin ya fitar a wannan makon, shin wadanne dalilai ke saurin raba masoya ?,
Shirin samartaka ya sami ra’ayoyi daban-daban, kama daga lamarin da ya shafi tarbiyya, kwadayi, kauna, son ganin ido, sa hannun iyaye, abokan zama, tarihin iyali, da sauran su.
Koda shike zamani ya sauya, ba kamar yadda lamarin yake a shekaru da dama da suka gabata ba, lokacin da iyaye ke ba ‘ya’yansu umurnin amincewa su auri wadanda suka tanada masu ko da basu taba zantawa da juna ba, ko kuma sun sani amma basa so.
Yawanci hakan na ci gaba da faruwa ba tare da wata matsala ba. Amma wannan zamanin ya yiwa waccan al’adar karan tsaye duk da cewa har yanzu ana samun al’amurra irin su, said dai ba duka aka jin labarin sub a..
A matsayin ka na uba ko uwa, ko matashi ko matashiyar da kuka sami kawunan ku a irin wannan hali, ina mafita?.
Dalili kenan da yasa muke son jin ra’ayoinku domin taimakawa dumbin jama’a da dama da suke bukatar muhimmiyar shawara domin kaucewa fadawa cikin hatsarin zama cikin irin wannan yanayin rayuwa.
Kuna iya bayyana ra’ayi a kowanne lakaci kuke bukata a shafin mu na yanar gizo mai adireshi wwwdandalinvoa.com ko shafin mu na sada zumunta mai adireshi voahausafacebook domin a bayyana ra’ayi.