Jami’ai a Freetown, babban birnin Saliyo sun ce akalla mutane 250 suka mutu sanadiyyar zaizayar laka da kuma ambaliyar ruwa.
A ranar Litinin, ‘yan uwan wadanda bala’in ya rutsa da su, sun yi ta tonon laka domin neman masoyansu, yayin da aka tura ma’aikatan soji domin su taimaka da aikin ceton.
Hotunan da aka yi ta sakawa a shafukan sada zumunta, ciki har da na bidiyo, sun nuna yadda mutanen yankin da lamarin ya faru, suna tafiya cikin lakar da ta kai har kirjinsu, suna laluben hanya.
Wannan bala’i da ya faru da safiyar ranar Litinin, ya biyo bayan ruwan sama da aka yi ta tafkawa ne kamar da bakin kwarya.
Shaidu sun ce hanyoyin yankin da bala’in ya faru, sun koma tamkar kogunan laka.
Wani mai magana da yawun kungiyar ba da agaji ta Red Cross, ya fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa sun tsamo akalla gawarwaki 312.
Hukumomi a kasar ta Saliyo, sun yi kiyasin cewa dubban mutane ne suka rasa muhallansu sanadiyar zaizayar lakar da ambaliyar ruwa.