Wadanda Suka Kai Hari Turkiya daga Kasashe Uku Suka Fito

Jerin wadanda suka rasa rayukansu a harin Turkiya

Gwamnatin kasar Turkiya tace harin nan da wasu ‘yan kunar baki wake su ukku su kai a tashar babban birnin kasar na Istanbul , sun fito ne daga kasashen Rasha,Uzbekisttan,da Kyrgyztan.

Jamian kasar suka ce sunyi imanin wannan harin da aka kai, ba kowa bane illa ‘yan kungiyar ISIS, sai dai basu bayyana sunayen wadannan mutanen ba.

Adadin mutanen da suka mutu kawowa yanzu sun kai 44 yayin da sama da 230 ne suka samu rauni daban-daban.

Sai dai ‘yan sanda sun kai samame a wurare har 16 a wasu wuraren dake makwabtaka da babban birnin kuma sun samu nasarar kame mutane har 13 ne da suke da alaka da kungiyar ta ISIS.

Jana'izar wadanda aka kashe a harin

Haka kuma kanfanin dillacin labarai mallakar gwamnati yace mahukunta sun kame wasu mutane 9 dake yammacin gabar kogin birnin Izmir wadanda ake zargi suma suna da alaka da kungiyar ta mayakan ISIS dake fada a kasar Syria, kuma sune ke mara wa kungiyar baya da kudi, sabbin sojoji da kuma sauran bukatun yau da kullun.