Wacce Rawa Malaman Addinai Za Su Iya Takawa a Zaben 2019?

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osibanjo, ya yi kira da shugabannin addinai da su yi wa kasar addu'a domin a yi zaben shekarar 2019 cikin lumana.

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osibanjo, ya yi kira ga shugabanin addinai a Najeriya da su yi wa kasar addu'o'i don a sami dawwamammen zaman lafiya kafin zabe, lokacin zabe, da kuma bayan zaben 2019.

Farfesa Yemi Osibanjo ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai wa taron mabiya darikar Ahmadiya na kasa ziyara, a garin Ilaro na jihar Ogun.

Osibanjo ya kara da cewa hanya daya da Najeriya da 'yan Najeriya za su sami ci gaba ita ce, dukkan 'yan Najeriya su kasance cikin zaman lafiya.

Don haka ya bukaci sauran addinai da su yi koyi da darikar Ahmadiyya a wajen kira ga zaman lafiya.

Shugaban darikar Ahmadiyya a Najeriya dokta Mashahud Fashola ya ce za su ci gaba da yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Saurari Rahoton Hassan Umaru Tambuwal:

Your browser doesn’t support HTML5

Wacce Rawa Malaman Addinai Za Su Iya Takawa a Zaben 2019? - 1'54"