Wa’azin Kungiyar Izala Na Kasa Na Wannan Shekarar

Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau

An kammala babban taron wa’azi na kungiyar Izala ta kasa da kasa baki daya a jihar Kano.

Taron dai ya sami halartar manyan Malamai da Shehunnai da dubban mabiya a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar mata a birnin Kano.

Batun kudurin dokat daidaita gado tsakanin jinsin maza da mata matsin tattalin arziki da al’umma ke ciki da jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin al’ummar musulmi suna daga cikin manyan batutuwan da suka mamaye wa’azin na bana.

Shugaban kungiyar Izala ta ‘kasa Imam Abdullahi Bala Lau, ya ja kunne ga ‘yan Majalisa game da dokar daidaita gado tsakanin maza da mata, ya kuma yi kira ga gwamnati domin daukar duk matakan da suka kamata don ganin an farfado da tattalin arzikin kasa baki daya.

Shima Sheikh Abdulwahab Abdullah cewa yayi duk musulmin Sanata da yayi shiru yana karbar albashi har aka tabbatar da dokar, tabbas hakan ya sabawa dokar Allah.

Mai taimakwa shugaba Buhari na musamman kan lamarin Majalisar wakilan Najeriya, Abdurrahman Kawu Sumaila, yace fadar shugaban kasa bata da hannu kan kudirin wannan doka. Ya kuma ce har yanzu shugaban kasa bai ma san da wannan doka ba, domin har yanzu bata karaso zuwa teburinsa ba.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Wa’azin Kungiyar Izala Na Kasa Na Wannan Shekarar - 3'09"