Soja Sun Ce Ba Su Hana Sauka Ko Tashin Jirgi A Maiduguri Ba

Jirgin fasinja yana sauka a filin jirgin Murtala Muhammed dake Lagos, Nigeria.

Shiyya ta 7 ta rundunar sojojin Najeriya, ta ce ba ta da masaniyar ko wanene ya bayar da umurnin hana sauka o tashin jiragen sama a babban filin jirgin sama na Maiduguri, jihar Borno, a ranar jumma'ar da ta shige.

Sojoji masu yawa sun bayyana a filin jirgin saman suka hana jigilar daruruwan mutanen dake shirin tashi domin tafiya Umrah, aka kuma hana wani jirgin dake dauke da uwargidan gwamna Kashim Shettima na Jihar borno iznin sauka na tsawon sa'o'i da dama.

Kakakin shiyya ta 7 ta rundunar sojojin, Kanar Mohammed Dole, yace rundunarsu ba ta da masaniya a kan ko wanene ya bayarda wannan umurni.

Amma sanata Mohammed Ali Ndume mai wakilar Borno ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya, kuma daya daga cikin masu niyyar zuwa Umrah da aka hana ma tashi, yayi tur da irin wannan abinda ya bayyana a zaman bakin iko, wanda yace ko a zamanin mulin soja ba a yin irinsa.

Wasu 'yan jihar ta Borno ma sun ja kunnen gwamnati da cewa duk abinda mutum ya shuka, shi zai girba.

Ga cikakken rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri...

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Soja Ta Ce Ba Ta San Wanda Ya Hana Sauka Ko Tashin Jirgi A Maiduguri Ba - 2'20