Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) na shirin bude sabon ofishi a shiyyar Arewa Maso Gabashin Najeriya.
Za a bude a ofis din ne a jihar Gombe, wannan kuma na daga cikin matakan fadada ayyukan VOA a kasar, a cewar hukumomin gidan rediyon.
Shugaban Sashen Hausa, Alhaji Aliyu Mustapha Sokoto, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ga gwamnan Jihar Alhaji Muhammed Inuwa Yahaya.
"Ofis ne da zai zo da gidan rediyo da talbajin a cikinsa, zai zama babban ofishinmu na shiyyar arewa maso gabashin Najeriya." Inji Mustapha.
Ya kuma shaida wa gwamna Yahaya cewa, dalilin da ya sa aka zabi Gombe shi ne, jihar ta kasance mahada ga jihohin yankin da dama.
Gombe jiha ce "da ke tsakiyar duk inda ka bullo wa sashen arewa maso gabashin kasar nan."
Ya kara da cewa, "sannan kuma Gombe tana kusa da dukkan dalilan da suka sa muke bukatar dasa ofishin nan, ma'ana; samun bayanai kan abin da ya shafi wannan yanki."
A nasa bangaren, gwamna Yahaya, ya nuna godiyarsa ga Muryar Amurka saboda zaben jihar Gombe ta kasance mai masaukin ofishin gidan rediyon na VOA.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad daga Gombe:
Your browser doesn’t support HTML5