An kammala shirin bada horo na musamman na kwana biyar ga daliban Jami’ar Bayero ta Kano kan amfani da fasahar aikin jarida da yada labarai wajen bunkasa sana’o’I da kasuwanci.
Gidan rediyon muryar Amurka ne ya dauki nauyin gudanar da taron inda aka zabo dalibai masu koyar aikin jarida a jJami’ar ta Bayero su fiye da talatin domin cin gajiyar shirin.
Wannan dai shine karo na biyu da gidan rediyon muryar Amurka ta bada makamancin wannan horo ga daliban dake koyon aikin jarda a Jami’ar Bayero.
Shugaban shashen hausa na muryar Amurka, Mr. Leo Keyan, ya ce taron na bana ya maida hankali ne akan harkar cinikayya, da kira ga ‘yan jarida dasu kara sa kaimi wajan neman sanin matsalolin da kamfanoni ke fuskanta.
Wasu daga cikin dalibai sun nuna farin cikinsu ga wannan horo da gidan rediyon muryar Amurka ya basu suna masu cewa horon ya canja masu tunaninsu.
Shugaban sashen koyon aikin jarida na Jami’ar ta Bayero, Dr. Sukeoiman Mainasara ‘Yar Adua, yace kwalliya ta fara biyan kundin sabulu game da wannan horo na VOA,
Malam Abubakar S D, daya daga cikin daliban da suka hallarci taron na bara wanda kuma tuni ya kammala karatun sa a Jami’ar ta Bayero, ya ce ilimin, daya samu a wurin horarawan na bara yanzu haka ya mallaki abinda nake da burin aiwatarwa watau kafa ta yada labarai mai suna “Labarai 24.com”.