Virgil Van Dijk Ya Zama Gwarzon Dan Wasan Firimiya Na Bana

An zabi dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Virgil van Dijk, a matsayin gwarzon dan wasa na kungiyar kwararrun 'yan kwallon da ke buga gasar firimiya na kasar Ingila a bana.

Virgil van Dijk mai shekara 27 ya doke, abokanan takararsa Raheem Sterling, Bernardo Silva, Sergio Aguero, Sadio Mane da kuma Eden Hazard,

Van Dijk ya karbi kambun ne daga hannun abokin buga wasansa na Liverpool Mohamed Salah, wanda a shekarar da ta gabata, 2017/18, shi ya lashe kyautar.

Bayan haka kuma Van Dijk ya kasance dan wasan baya na farko da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan ta kungiyar kwararrun 'yan wasan da ke buga firimiya tun bayan da dan wasan baya na Chelsea John Terry da ya lashe a 2005.

Dan wasan ya buga dukkanin wasannin da Liverpool ta fafata a gasar a kakar bana inda take matsayi na biyu a gasar firimiya lig mako na 36 banbancin maki 1 tsakanita da Manchester City wacce ta ke na daya, ya ci kwallaye uku a wasannin bana ya taimaka wajan shan 2, bayan haka kuma ya tallafa wa kulob din ya kai wasan daf da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai Uefa Champion League bana a ranar 1 ga watan Mayu 2019 zata gwabza da Barcelona a Camp Nour.

Dan wasan ya ce wannan ita ce kyauta mafi girma da dan wasa zai samu wacce abokan buga wasansa suke zabe duk karshen kakar wasa.

A bangaren matasa kuwa, Raheem Sterling ne ya lashe kyautar gwarzon

matashin dan wasa na Firimiya bana, inda a bara dan wasan Manchester City Leroy Sane ya lashe kyautar.