Victor Osimhen Yana Kan Gaban Idon Wasu Kungiyoyin Turai

Rahotanni sun nuna cewa dan wasan Super Eagles Victor Osimhen yana kan gaban idon wasu kungiyoyin Turai da dama a yanzu ciki har da Newcastle da Barcelona wadanda suka shiga tseren don su kwato dan kwallon Super Eagles din.

A farkon makon, labari ya bulla cewa Barcelona ta tsallake a gaban jerin kungiyoyi da ke neman su dauke Osimhen daga Lille.

Osimhen ya ji daɗin nasara a kakar wasa ta bara a Charleroi inda ya zira kwallaye 20 a raga a karon farko a Belgium.

Lille ta cafke dan shekara 20 din ne cikin sauri a lokacin bazara a madadin dan kasar Portugal Leao wanda ya koma AC Milan.

Amma ana yawan kwatanta tsohon dan wasan Wolfsburg din da dan wasan Nicolas Pepe wanda ya tafi Arsenal a kan kudi fam miliyan 72, yayin da ya zira kwallaye takwas a wasanni 11 da ya bugawa Laliga 1 a kakar wasan bana.

Osimhen ya koma Lille ne daga Charleroi ta Belgium kan kudi fan miliyan 10.8.

Saboda tsabar kwarewarsa a Faransa, kuma a gasar zakarun Turai ta UEFA a kwanan nan, shi ya tilastawa shugaban kungiyar daukar ma'aikata Steve Nickson da tawagarsa suka hada da Osimhen a cikin jerin waddan da za su dauka.

Kocin Newcastle Steve Bruce zai samu kudin da zai kashe a watan Junairu akan wannan lamarin, abin da zai bashi damar ya kulla yarjejeniya da dan kwallon Najeriya idan ya yiwu.